1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikas ga shari'ar shugaban Kenya

December 20, 2013

Cece-kuce game da bukatar dage shari'ar shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a kotun ICC.

https://p.dw.com/p/1Ae5q
Kenia Präsident Kenyatta und Vizepräsident Ruto
Hoto: picture alliance/dpa

Kwararru da kuma wasu 'yan kasar Kenya na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu dangane da bukatar da babbar mai gabatar da kara a kotun ICC ta hukunta manyan laifukan yaki dake birnin The Hague, Fatou Bensouda ta gabatar, ta neman alkalan kotun su jinkirta shari'ar da take yi wa shugaban Kenya Uhuru Kenyata, saboda abin da ta danganta da rashin wadatattun shaidu. Ta ce daya daga cikin masu bayar da shaida ya nuna rashin sha'awar ci gaba da bayar da shaida, yayin da dayan kuma ya karyata kansa da kansa dangane da shaidar da ya gabatar wa kotun. A cewar, George Musamali, kwararre a harkokin da suka shafi kotun ta ICC da ke birnin Nairobin kasar ta Kenya - cikin zantawarsa da tashar DW, sam sam basu yi mamakin wannan matsayin ba, kasancewar, kabilu biyun da suka yi fito na fito a lokacin rikicin, a yanzu su ne ke jan ragamar mulkin kasar:

Ya ce " Mun lura da cewar, a yayin da shari'ar ke gudana, masu gabatar da kara na ci gaba da janyewa. Saboda haka, babu yadda za a yi shari'ar ta ci gaba sakamakon rashin shaidu."

Kwararren dai, ya ce tunda bangarorin da ya kamata su bayar da shaida akan junansu ne ke mulki, to, kuwa akwai yiwuwar su shawo kan masu gabatar da shaidar su janye daga karar, wanda ya ce, ba za a yi wa wadanda rikicin da ya biyo bayan zabukan kasar a shekara ta 2007 da kuma 2008 adalci ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Usman Shehu Usman