Cikas a yaki da cutar Ebola
September 21, 2014Talla
Kungiyar Agajin gaggawa ta Red Cross ta nemi da gujewa kai hari kan jami'an kiwon lafiya a kasashen da cutar Ebola ta shafa. Wannan kiran ya zo ne bayan da wasu gungun mutane a kasar Saliyo suka kai fafari wasu jami'an kiwon lafiya a wajen jana'izar wani mai dauke da cutar ta Ebola a kasar Saliyao- Daya daga cikin kasashen da suke fama da cutar ta Ebola.
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon cewa ya yi: "A kowace rana sai kara samun wadanda suka kamu da cutar da wadanda ke mutuwa ake samu, domin haka ya zama wajibi mu yi tsayin daka domin ko ya ba da taimako ta yadda za shawo kan saurin yaduwar cutar"
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo