1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawana ta musanman tsakanin Xi da Poutine

March 21, 2023

A ci gaba da ziyarar kwanaki uku da ya kai Rasha, shugaban kasar Chaina Xi Jinping zai yi ganawa ta musanman da takwaransa Vladimir Putin a wannan Talata.

https://p.dw.com/p/4Oy9G
Shugaban Chaina da na Rasha a MoscowHoto: AP Photo/picture alliance

Shugannin biyu za su gana ne yayin da a daya gefe shugaban gwamnatin kasar Japan wacce a cikin watan Fabarairun da ya gabata ta sanar da tallafin biliyan biyar da rabi na dalar Amurka wa Ukraine zai isa birnin Kiev.

Yayin da yake tsokaci kan ziyarar ta Xi, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Chaina za ta fake ne da diplomasiyya don kara karfafa wa Rasha guiwa a ci gaba da aikata manyan lefukan yaki da ta ke yi a Ukraine.

To sai a game da batun ba da sammacin kama mista Putin da kotun kasa da kasa mai hukunta masu manyan laifuka ICC ta yi, ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta bukaci kotun da kada ta saka siyasa a lamarin kana kuma ta mutumta rigar kariyar shugannin kasashe.