'Yan bindiga na ci gaba da kai hari a Katsina
June 25, 2020Rahotannin dake fitowa daga Arewa maso yammacin Najeria na cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da hallaka mutane bakwai ciki haa da wani jami'in tsaro a lokacin wani hari da 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Danmusa da ke jihar ta Katsina a daren Laraba washe garin Alhamis.
SP Isa Gambo kakakin rundunar 'yan sanda na Jihar ta Katsina ya shaida wa DW cewa da minsalin karfe biyu na cikin daren Laraba 'yan bindigan suka kai hari a wasu kauyika biyu na Kanawa da Kanga na karamar hukumar Danmusa inda suka kashe mutun shida suka kuma raunata biyar.
A baya dai maharan sun saba kai hare-haren kan babura amma yanzu sun canza saban salo wanda har ya ba su damar halaka wani jami'an tsaro a lokacin da jami'an tsaran da aka jibge a yankin ke kokarin kare al'umma daga harin a cewar SP Gambo
Kakakin Rundunar 'yan sandan ya ce tuni an tura da dakarun tsaro yanki dan gano maharan.
Wannan hari dai ya shafi wasu iyalan gida daya inda take aka halaka masu mutum uku a cewar wannan daga cikin mambobin wannan gida wanda amma shi ya yi nasarar ketara rijiya da baibai. Akwai kuma wasu mata biyu kishiyoyin juna wadanda 'yan bindigar suka harba da bindiga tare da raunata su, kuma yanzu haka suna kwance a babban asibitin garin na Danmusa inda suke karbar magani.
Ci gaba da kai wadan nan hare-hare na zuwane bayan ziyarar da wasu manyan jami'an kasar suka kai jihar ta Katsina inda suka sha alwashin gami da nuna fushi kan yadda ake tafiyar da lamuran tsaro a kasar da Shugaban Buhari ya bayyana, da amma har kawo yanzu al'umma na ci gaba da zura Ido, abin da ya fara tunzura kungiyoyi soma gudanar da zanga-zangar lumana.