1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da tsare yan adawa a kasar Chadi

May 16, 2013

Wakilin DW a Ndjamena na daga cikin wadanda aka tsare bayan da aka zargi yan adawa da yan jarida da laifin neman kayar da gwamnatin shugaban kasa Idriss Deby

https://p.dw.com/p/18ZKj
Hoto: picture-alliance/dpa

A kasar Chadi, gwamnati tana daukar matakai masu tsanani kan yan adawa da masu ilimi da kuma yan jaridu. A farkon watan Mayu gwamnatin tace ta dakatar da wani yunkuri da aka yi na juyin mulki, abin da ya sanya gwamnatin ta shiga kama  mutanen da ta zargesu da hannu a wannan yunkuri, ciki har  har da wakilin DW a birnin Ndjamena. A daya hannun kuma,  kasar dake tsakiyar Afrika, tana taka muhimmiyar rawa a rikicin kasar Mali.  Chadin ta tura runduna mafi girma ta nahiyar Afirka da ta kunshi sojoji  kimanin 2000, domin taya Faransa yaki da yan tawaye a kasar ta Mali.

Ba zato ba tsammani  shugaba Idris Deby ya maida ranar Litinin da ta wuce ta zama ranar hutu a kasa baki daya, saboda a wannan rana  kashi farko na sojojin Chadi 700 suka koma gida daga Mali, abin da ya baiwa mazauna  Ndjamena, babban birnin kasar ta Chadi damar fita kan tituna domin  marhabin da farin cikin komowarsu. In banda wannan biki, yanzu dai Chadin bata da wani abin da zata yi farin cikinsa a kasar. Tun farkon watan Mayu an kama mutane tsakanin 10 ne zuwa 20. Zargin da ake masu shine wai sun hada baki a yunkurin aiwatar da juyin mulki ga gwamnatin shugaban kasa Idriss Deby. Daga cikin wadanda aka kama har da yan jarida, kamar  wakilin DW Eric Topona da kuma dan majalisar dokoki na yan adawa, Gali Gata Ngote, da takwaransa, Routouang Yora Golom, wanda ma wakilin gwmnatine a majalisar dokokin.

Yar gwagwarmayar kare hakkin yan Adam kuma lauya Delphine Djiraibe, tana daya daga cikin lauyoyin dake kare yan majalisar dokokin guda biyu. Tayi korafin cewar wadannan yan majalisa biyu an kama su ne duk kuwa da  kariyar da suke da ita.

Tschadische Soldaten bei Rückkehr aus Mali 13.05.2013 mit Präsident Idriss Deby Itno
Farin cikin komawar sojojin Chadi gida daga MaliHoto: STR/AFP/Getty Images

Matakin da ake dauka gaba daya kan wadannan mutane ba daidai bane. Wadannan mutane tilas ne a sake su. Duk da haka an gabatar masu da  takardun da suka bada izinin ci gaba da tsare su, saboda haka har yanzu suna jira a kaisu gaban alkali da zai binciki laifukansu. Tun da kuwa  alkalai masu binciken farko na masu laifi a Chadi ba tilas  bane su kiyaye wa'adin sauraron wanda ake kara, saboda haka ana iya daukar lokaci mai tsawo  a wannan al'amari.

Kungiyoyin kasa da kasa suma dai sun nemi  yiwa wadannan mutane da aka kama shari'a ta gaskiya, sun kuma baiyana mamakin dalilai dabam dabam da aka kama mutanen karkashinsu. Helga Dickow, masaniya ce kan kasar Chadi, a cibiyar Arnold Bergstresser dake jami'ar Freiburg a nan Jamus. Tace a zatonta, shugaban na Chadi yana amfani da aiyukan sojojinsa ne a Mali da kuma yabon hakan da yake samu a ko ina cikin duniya, domin cimma burinsa. Shugaba Idriss Deby dai yau shekaru 20  yana shugabancin Chadi da hannun karfe. Shi kansa ya karbi shugabancin ne a shekra ta 1990 ta hanyar juyin mulki. Tace bai zama abin mamaki ba ganin cewar wakilan gwmnati ma suna daga cikin wadanda aka kama kuma suke tsare, saboda ba dukkanin wakilan gwamnatin ne suke goyon bayansa ba. Shugaba Deby ya musunta cewar yana farautar yan adawa. A makon jiya Faransa tayi sharhin farko game da mutanen da aka kama a Chadi, inda ma'aikatar harkokin waje tace ta damu a game da kame-kamen da ake yi a Chadin, kuma wadand suke tsare ya kamata ko dai a sak su ko a gaggauta yi masu shari'a.

Eric Topona
Wakilin DW a Ndjamena Eric ToponaHoto: DW

Mawallafi: Müller/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman