China: karshen dokar killacewa
December 26, 2022Talla
Hukumomin kiwon lafiya na kasar sun ce daga ranar takwas ga watan Janairu za a fara aiwatar da dokar bayan da aka dage yawancin matakan yaki da COVID-19 da ke aiki ,a farkon watan Disamba. Daga wata mai zuwa gwajin daya ne kawai na kasa da sa'o'i 48 za a bukata daga matafiyi kafin shiga China. Kasar China ita ce kasa daya tilo mai karfin tattalin arziki da ta ci gaba da sanya dokar hana zirga-zirga da kuma killace baki 'yan yawan shakatawa da ke shiga kasar saboda karuwar cutar corona da ake samu a kasar a baya-baya nan.