NATO na ingiza mambobinta zuwa yaki
July 12, 2023Talla
Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta China ya nunar da cewa, kungiyar Tsaron ta NATO ta gaza tantance abin da yake daidai da kuma wanda ba daidai ba. Ya kara da cewa kungiyar na daukar wasu matakan da ba su dace ba, wanda kuma tuni China ta sa kafa ta yi fatali da su. A cewarsa duk da NATO ta yi ikirarin cewa ita mai bayar da kariya ce, amma tana zuga mambobinta su yi ta kashe kudi a fanonin sojansu da fadada karfin ikonsu a kan iyakoki. Kana ya yi zargin NATO din da ingiza mambobin nata, su je takalar fada ko fito na fito a yankin Asia da Pacific.