1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta yi watsi da sammacin ICC na cafke Al-Bashir

Sadissou YahouzaJuly 22, 2010

Duk da sammacin kotun ICC, shugaba Omar Hasan El-Bashir na Sudan ya halarci taron CEN-SAD a ƙasar Chadi

https://p.dw.com/p/ORLf
ICC ta bada sammacin cafke shugaba Omar Al-BashirHoto: picture-alliance/dpa/Montage DW

Ƙasar Chadi, ta yi watsi da kiran kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta lefikan yaƙi wato ICC ,na cafke shugaban ƙasar Sudan Omar Hasan El-Beshir, domin tasa ƙeyarsa zuwa birnin the Hague ko kuma la Haye, inda kotun ke buƙatar gurfanar da shi ,bayan zargin da ta yi masa, na aikata kisan ƙare dangi a yankin Darfur.A yanzu haka dai shugaba Al-Bashir, na cikin ziyara  a birnin N´Djamena na ƙasar Chadi. inda ya ke halartar taron shugabanin ƙasashen Ƙungiyar CEN-SAD. Wannan shine karon farko da ya sa ƙafa  cikin wata ƙasa memba a kotun ICC,tun bayan da kotun ta bada saban sammacin sa  a watan da muke ciki.

Ƙasar Amirka ta yi kira ga hukumomin Chadi a kan yaunin da ya rataya kansu na mutunta yarjejeniyar da su ka rattaba hannu ta amincewa da dokokin kotun ICC, saboda haka a cewar Amirka cilas, N´Djamena ta cafke shugaba Omar E-Beshir.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita Umaru Aliyu