SiyasaAfirka
Chadi da Mauritaniya sun rusa G5 Sahel
December 13, 2023Talla
Kasashen biyu da suka rage a cikin kawance tsaron kungiyar G5 Sahel, Mauritaniya da Chad sun amince da rusa kungiyar baki daya, wadda aka kafa da nufin yaki da kungiyoyi masu nasaba da Jihadi, bayan kasashen uku na Burkina Faso da Mali gami da Jamhuriyar Nijar sun fice tun da farko daga cikin kungiyar.
Karin Bayani: Nijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a Sahel
A shekara ta 2014 aka kafa kungiyar mai mambobin kasashe Mauritania, Chad, Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar. Juye-juyen mulkin soja da aka samu a kasashe uku na Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar sun janyo cikas kan tafiyar da aikin kungiyar musamman na samun tallafi daga kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya.