Cece kuce game da kame ɗan Boko Haram a Maiduguri
October 23, 2012Wannan taƙaddama dai ta faro ne bayan da rundunar tabbatar da tsaro da wanzar da lafiya da aka fi sani da suna JTF ta fidda sanarwa da ta ce ta kame wani babban kwamandan yaƙi na ƙungiyar Jama'atu Ahlulsunna lilda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram a gidan wani ɗan majalisar dattawa a garin Maiduguri.
Duk da cewa dai rundunar JTF ba ta fayyace sunan ɗan majalisar dattawan da ta ce ta kame Shu'aibu Muhammed Bama kwamandan ƙungiyar nan Mai gwagwarmaya da makamai a arewacin Najeriya ba, Sanata Ahmad Zanna ya gaggauta kiran taron manema labarai inda ya ce ba'a kama ɗan Boko Haram a gidansa ba.
Ƙoƙarin wanke kai
Bayan nan ne kuma ya sake kiran taron manema labarai inda ya shaida musu cewa lallai Shu'aibu Bama ɗan 'yar uwarsa ne amma bai san ko ɗan ƙungiyar Boko Haram ba ne kuma a cewar sa tsohon gwamnan da ya kayar a zaɓe ne wato Ali Modu Sherif ya ke son shafa masa kashin kaji ta hanyar amfani da rundunar ta JTF.
Sai dai a wani martani da ya mayar ta bakin kakakinsa Alhaji Umar Duhu, tsohon gwamnan Sanata Ali Modu Sherif wanda zamanin sa ne aka fara faɗa da ƙungiyar gwagwarmayar ya ce lallai Sanata Zanna ya taimaka wa ƙungiyar Boko Haram don kuwa ya ɗauki wasu matasa da ya horar kuma a cewar sa an bi diddigi an samu sun je samun horo a Afghanistan da Siriya.
Alhaji Umar Duhu ya ƙara da cewa zaman sa da ɗan majalisar dattawa na biyu daga jami'iyya PDP da aka samu da tallafa wa ƙungiyar Boko Haram ya tabbata cewa jam'iyyar ita ce ke da hannu a yawancin tashe-tashen hankulan da ake dangantawa da Jama'atu Ahlulsunna musamman a Maiduguri.
Zargi juna a kan tallafa wa 'yan bindiga
Wannan ce-ce-ku-ce dai ya buɗe sabon shafi ga mahawara da ake yi kan su waye ke goyon bayan ƙungiyar gwagwarmayar kamar yadda aka yi hukumomi da sauran ɗai-ɗaiku ke zargi wasu ‘yan siyasa na da hannu a rikicin duk da cewa ƙungiyar Jama'atu Ahlulsunna ta sha musanta hakan.
Talakawa kamar Comrade Garba Tela Herwa Gana Wudil Gombe na ganin asiri ne ya fara tonuwa tsakanin shugabannin arewacin Najeriya da suka ja baki su suka yi shiru kan bala'in da ya afka wa yankin.
Yanzu haka dai Sanata Ahmad Zannan na shan tambaya a hannun jami'an leƙen asiri na SSS inda wasu ‘yan ƙasar ke ganin ya kamata shima tsohon gwamnan a gayyace shi don amsa tambayoyi kan haƙiƙanin al'amarin da suke zargin juna a kai.
Mawallafi: Amin Suleiman Mohammed
Edita: Mohammad Nasiru Awal