Bush ya gana da Ban Ki Moon
January 17, 2007An yi ganawar farko, tsakanin saban sakatare Jannar na MDD Ban Ki Moon, da shugaba Georges Bush na Amurika, a birnin Washington.
Saban sakataren, ya bayyana aniyar ci gaba da ɗasawa da Amurika, a tafiyar da harakokin mulkin sa, ba tare da ya yin wasti da sauran ƙasashe ba , membobin Majalisar.
Ya kuma yi kira ga gwamnati Amurika, ta ƙara yawan tallafin kuɗaɗe da ta ke badawa ga Majalisar Dinkin Dunia.
A ɗaya wajen kuma, ya bukaci Amurika, ta shiga member, a hukumar kare hakkokin bani adama ,ta MDD da ta ƙauracewa ya zuwa yanzu.
Sannan ya taɓo batutuwa daban-daban da su ka shafi rikicin gabas ta tsakiya, Corea ta Arewa da Darfur.
A game da rikicin Darfur shugaban Amurika, ya yi yabo a kan yadda Ban Ki Moon, ya duƙufa wajen warware wannan rikici.
Bugu da kari Georges ya ce ba shi da kwankwanto, wajen ƙwazo da hazakar Ban Ki Moon, wanda za su bashi damar fuskantar ƙalubalen da zai ci karo da shi a saban muƙamin nasa.