1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ta haramta luwadi da madigo

July 11, 2024

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta amince da kudurin dokar ne da ya ayyana dukkan ayyukan 'yan luwadi da madigo a matsayin babban laifi a kasar bayan ganawa da masu ruwa da tsaki.

https://p.dw.com/p/4iAjK
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim TraoreHoto: Donat Sorokin/TASS/dpa/picture alliance

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso  ta ce ta amince da wani kuduri da zai ayyana auren jinsi a matsayin babban laifi a kasar.

Kasar dake yammacin nahiyar Afrika ta bi sahun kasashe 22 cikin 54 na nahiyar ta Afrika da suka haramta aure ko neman jinsi guda da ya kasance laifi da zai kai ga kisa ko dauri na dogon lokaci.

Burkina Faso dai na karkashin mulkin soji tun a shekarar 2022 sannan kasar na cikin kawancen gwamnatocin soji da take makwabtaka da su na Mali da Nijar.

Mali da Nijar da Burkina sun juya wa ECOWAS baya

Dukkan kasashen uku sun ki gudanar da zabe sannan sun juya wa abokansu na da wato kasashen yamma baya.

A wata sanarwa da gwamnatin sojin ta sanya wa hannu ranar Alhamis, ta ce daga yanzu duk ayyukan 'yan luwadi da madigo babban laifi ne kuma doka za ta hukunta duk wanda ta kama da aikatasu.