Dakon yadda za ta kaya a shirin kama al-Bashir
June 15, 2015Talla
Shugabannin kassahen Afrika na kammala taron kolinsu yayin da batun sammacen kama shugaba Omar al-Bashir, da kotun ICC ke nema ya dauki hankali a wajen taron AU bayan da wata kotu a kasar ta Afrika ta Kudu ta nemi kada ya fita daga kasar.
A cewar Kamal Ismail, ministan kasa a ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta Sudan, wannan bukatar kotu babu wani tasiri da za ta yi babu kuma wata baraza da shugaban nasu zai fuskanta za su koma gida lafiya.
Wasu lauyoyi ne dai suka gabatar da wannan bukata a kotu inda suka bukaci gwamnatin wannan kasa ta mika shugaba al-Bashir ga kotun ta ICC. Sai dai babu wasu alamun cewa gwamnatin na da niyyar mika shi bayan da ta bayyana shi a matsyin bakonta da ke halartar taron na AU.