Bunkasa ma'adanan karkashin kasa a Najeriya
January 9, 2018Yanzu haka hukumomi da kungiyoyin masu haka da sarrafa ma’adanai a Najeriya suna kan hobbasa wajan karkato da akalar samun kudin shiga wa kasar zuwa ga bangaren dumbin albarkatun kasa da Allah ya hore wa Najeriya.
Sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya wanda Najeriya ta dogara da shi wajen samun kudin shiga tun bayan da kasar ta sami man fetur din a 1970, yanzu haka hankali ya fara karkata ga arzikin karkashin kasa wadanda kasar bata maida hankali akansu ba a baya. Jihar Bauchi na daga cikin wuraren da ke da nau’in albarkatu daban daban. Isah Muhammad Tahir shine shugaban wani kamfanin hakar ma’adanai na jihar Bauchi.
Karancin kayan aiki na zamani shine abinda ke kawo koma bayawajen aikin hakar ma’adanan a cewar shugaban gamayyar kungiyoyin masu hakowa da kuma sarrafa ma’adanan a jihar Bauchi Bello Inuwa Galoji.
Gambar Lere a karamar hukumar Tafawa Balewa na da tarin albarkatun Kuza wanda idan aka samar da kyakkyawar tsari zai taimaka wajen samar wa matasa ayyukan yi da kuma bunkasa arzikin yankin da ma kasa baki daya.