1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya yi gargadi kan watsi da ‘yan gudun hijira

November 30, 2016

A cewar shugaban Najeriya idan aka tilasta wa wadanda suka rasa gidajensu komawa garuruwansu ba tare da sake gina yankunansu ba, akwai yiwuwar wasunsu za su shiga wani halin da ke iya zama ta’addanci. 

https://p.dw.com/p/2TX6T
Nigeria Präsident Buhari empfängt befreites Schulmädchen Amina Ali
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Shugaban Muhammadu Buhari ya ce dole sai an sake gina makarantu da asibitoci gami da gidaje, domin ‘yan gudun hijiran su koma gida don sake sabuwar rayuwar, Inda ya ce in ba haka ba nan gaba za su iya zama bata gari wanda zai iya kaiwa ga shigarsu Kungoyoyin ‘yan gwagwarmaya. Don haka Buhari, ya ce ya zama dole gwamnati ta dauki malamai da za su koyar a makarantun da za a gyara domin cike gurbin malamai da aka halaka. 

Dama dai masana sun yi irin wannan gargadi a baya, inda suka ce yadda ‘yan gudun hijiran ke zube ba tare da samun abin yi ba, wanda zai samar da taro ko sisi domin dogaro da kai, hakan zai iya jefasu munanan hali. Furucin shugaba Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa za ta kwashe ‘yan gudun hijira domin maida su garuruwarsu a tsakiyar shekara mai zuwa.  A cewar ‘yan gudun hijiran da suka shafe shekaru biyu rabonsu da gidajensu, a maida su garuruwansu shi ne babbar bukatarsu a halin yanzu.

Masharhanta  sun nemi ayi taka tsan-tsan da daukar wannan mataki don gudun yin kitso da kwarkwata, a cewarsu kamata ya yi a nemi hanyar taimakawa wadannan ‘yan gudun hijira tare da koya musu sana’o’i, domin dogaro da akida kuma a karfafa koyar da ‘ya‘yansu karatu. Ko a sansanoni ne ta haka ne a cewarsu za a kaucewa su shiga ayyukan bata gari.