Buhari ya sha rantsuwar wa'adin mulki na biyu
May 29, 2019Talla
A ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2019 Shugaba Mohammdu Buhari ya sha rantsuwar fara wa'adin mulki na biyu na wasu shekaru hudu. Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar na cike da fatan mataki na gaba na samar wa kasar mafita kan tarin matsaloli da ake fama. Shugaba Buhari mai shekari 76 na ikirarin karya lagon mayakan Boko Haram a wadin mulkinsa na farko, sai dai 'yan adawa na kalubalantar nasarar shugaban a wannan bangare.