Buhari ya nemi 'yan takara da su yi murabus
May 11, 2022Talla
A wannan Larabar, fadar gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar inda a ciki ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga duk masu son shiga takara a zaben kasar na badi da ke rike da mukamin gwamnati, da su gaggauta yin murabus, shugaban ya nemi a mutunta wannan umarni da wa'adinsa ke cika a ranar sha shida na wannan watan Mayun 2022.
An jima ana tafka mahawara a cikin kasar kan wannan batu na son ganin ma'aikatan gwamnati musanman ministoci da suka shiga takara a zaben 2023 da ke tafe, sun soma ajiye mukaminsu tun da sun baiyana aniyarsu ta takara. A farkon shekarar 2023 miliyoyin 'yan Najeriya za su fita rumfunan zabe don kada kuri'arsu a zaben 'yan majalisu dana gwamnoni da kuma na shugaban kasar.