1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC ta gudanar da taron gaggawa

Zainab Mohammed Abubakar
February 18, 2019

Shugaba Mohammadu Buhari na Najeriya ya ce ya umurci sojoji da jami'an 'yan sandan kasar da su harbe har lahira duk wanda aka kama yana satar akwatin zabe ko kuma haifar da tsaiko

https://p.dw.com/p/3DcHk
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

A taron gaggawa da ya gudanar da manyan 'yan jam'iyyarsa ta APC a Abuja, Buhari ya ce zai tabbabar da cewar an gudanar da zaben da ak dage da mako guda, ba tare da wata matsala ba.

Shugaban Najeriyar ya ce baya saran wani zai kawo tashin hankali, amma duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ko kuma satar akwatin zaben, to wannan shi ne zai zame masa karo na karshe da zai aikata irin wannan laifi na taka doka.

Jam'iyyar APC mai mulki da ta adawa ta PDP dai na cigaba da zargin juna da shirya magudi, wanda wasu ke dangantawa da dalilan dage zaben na karshen mako da mako guda.