Ntaganda zai san makomarsa a kotun ICC
September 2, 2015Tshohon jagoran 'yan tawaye a kasar Kwango Bosco Ntaganda da aka fi sani da "Terminator" a ranar Laraban nan a gaban kotun ICC mai hukunta manyan laifuka zai san makomarsa bayan zarginsa da laifuka da suka hadar da aikata fyade da sanya kananan yara cikin ayyukan soja karkashin dakarunsa na 'yan tawaye.
Bosco jagoran 'yan tawayen a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango da ya mika kansa a shekarar 2013 ana tuhumarsa da aikata laifuka 18 na yaki da take hakkin bil Adama a wata shari'a da aka dade ana jimirin ganinta musamman a tsakanin al'ummar kasar ta Kwango wadanda ke cike da muradin ganin ya fuskanci hukunci a wannan kotu ta kasa da kasa da ke a birnin The Hague.
Kamar yadda 'yan fafutikar kare hakkin bil Adama ke cewa mutane 60,000 sun hallaka tun daga 1999, da fada ya tsananta a Gabashin Kwango.