1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon dan tawayen Kwango Ntaganda ya sake hallara a ICC

September 30, 2016

Bayan da kotun hukuntan manyan laifukan yaki ta The Hague ta amince mai dakinsa ta ziyarceshi ne tsohon shugaban 'yan tawayen Kwango Bosco Ntaganda ya jingine yajin cin abinci da yake yi don hallara a gabanta.

https://p.dw.com/p/2Qm8Z
Bosco Ntaganda Prozess ICC Den Haag 10.01.2014
Hoto: Reuters

Tsohon shugaban 'yan tawayen Kwango Bosco Ntaganda ya sake hallara a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya da ke birnin The hague, bayan da ya kawo karshen yajin cin abinci da ya shafe makonni biyu ya na yi. A baya dai ya nunar da cewa a shirye yake ya bakwanci lahira saboda kotun ta kasa da kasa ba ta yi masa shari'ar adalci, baya ga adawa da yake yi da yanayin da yake tsare a gidan yari.

Lawyan da ke kare Bosco Ntaganda ya bayyana cewar kotun The hague ta amince da bukatunsa inda ta amince mai dakinsa ta rinka kai masa ziyara. Shi dai Ntaganda ya yi watsi da laifuka 13 da ake zarginsa da aikatawa ciki har da kisan kare dangi da fyade a yankin Ituri na Kwando Dimukaradiyya tsakanin shekaru 2002 i zuwa 2003.

Bosco Ntaganda ya kasance mutumin da ya fara yajin cin abinci a gidan yarin kotun duniya The hague. sai dai ana zargin kungiyar FPLC da ya shugabanta da zama uwargami a rikicin kabilanci da ya salwantar da rayukanku mutane dubu uku a yankin Arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyar Kwango.