Boris Becker: Hotunan tarihin rayuwarsa
Gwarzo, mai barkwanci, mai kazar-kazar - Dan wasan tennis Boris Becker bai bar komai ba a rayuwarsa. Amma wata kotu a Landan ta same shi da laifin nuku-nuku da bayanan kadarorin da ya mallaka.
Yadda "Bobbele" ya zama gwarzon tennis
Sama da Jamusawa miliyan 11 ne suka yi ta murna a ranar 7 ga watan Yulin 1985 a gaban talabijinsu, lokacin da wani dan wasan tennis mai shekaru 17 wato Boris Becker ya zama fitacce a wannan fage. Nasarar da "Bobbele" ya yi a Wimbledon ya haifar da habakar wasan tennis a Jamus. Sannan shekara guda bayan haka da kuma a shekarar 1989 ya sake yin nasara.
Becker ya bude sabon babi
Jamus ba ta taba lashe kofin wasan tawaga na tennis ba har sai da Boris Becker ya gawurta. A wasan karshe na gasar cin kofin Davis, Becker da Carl-Uwe Steeb (dama.) sun yi nasara sau biyu a kan ’yan wasan tennis mafi tashe a duniya a lokacin: Mats Wilander na daya a duniya da dan wasan Wimbledon Stefan Edberg. Becker ya sake bayar da gudunmawa wajen samun nasarorin guda biyu a 1989 da 1993.
Salon wasan Becker
A shekarar 1990, an sake zaban Becker "Gwarzon dan wasa na shekara" a karo na hudu. Becker na iya habaka wasansa tare da canza shi cikin hanzari a filayen wasanni - musamman a kan ciyawa. Karfinsa shi ne: iya yin wasa ta sama. Magoya bayansa suna son Becker saboda salon wasansa - da tsalle tamkar dan wasan raga.
Ya samu zinare ta Olympics
A gasar Olympics ta 1992 a Barcelona, an fitar da abokan hamayyar na Jamus biyu Michael Stich (a hagu) da Boris Becker da wuri a wasanninsu. Sai dai a wasan tawaga, sun samu damar samar wa Jamus lamba mai daraja - zinare suka samu: "Ba mu yi magana da juna a zahiri ba saboda ba mu son juna sosai," in ji Becker bayan nasara.
Auren Becker na farko
A karshen 1993 Becker ya auri 'yar fim da zane-zane 'yar Jamus da Amirka Barbara Feltus. A shekarar 1999, lokacin da take da juna biyu na danta na biyu, ita da magoya baya sun gano badakalar biye-biyen mata a waje na Boris Becker ciki har da 'yar Rasha Angela Ermakowa. Sakamakon haka Becker ya samu 'ya da ita, wato haihuwa ta uku, kuma a 2001 ya saki Barbara.
Wasan Becker na karshe
Bayan shan kayen da ya yi a wani zagaye na gasar Wimbledon a hannun Patrick Rafter na Australiya a watan Yunin 1999, Boris Becker ya yi ritaya. A yanzu, Becker ya ce yana fama da rashin lafiya: "Na ji rauni a kugu. Ina da karfe mai tsayin santimita goma a idon sawun dama, ina dan dingishi."
Hukuncin farko na kotu ga Becker
A shekarar 2002, an yanke wa Becker hukuncin shekaru biyu na daurin talala bisa laifin kauce wa biyan haraji na Yuro miliyan 1.7. A cewar kotun dai, a hukumance Monaco ya kasance garin da Boris Becker ke da zama kuma yake biyan haraji tsakanin 1991 zuwa 1993, amma a hakika cibiyar rayuwarsa ta kasance a Munich.
Hukunci na biyu ga Becker
Boris Becker na da alhakin yin nuku-nuku da bayanan kadarorin kamfanin Sportgate, wanda ya mallaki kashi 60 cikin 100 na hannun jari - amma aka samu karamin adadi sabanin yadda aka bukata. A shekara ta 2007, kotu ta yanke masa hukuncin biyan Yuro 114,000.
Bikin aurensa na biyu
Boris Becker ya yi bikin aurensa na biyu a shekara ta 2009 tare da 'yar kasar Holland Sharlely Kerssenberg. Amadeus Benedict Edley Luis, shi ne ya zama da na hudu na Boris Becker. Ma'auratan biyu suna zaune ne a biranen Landan da Zurich.
Sabon aikin horaswa
A karshen 2013, labarai sun mamaye duniyar wasanni: Boris Becker ya zama babban kocin Novak Djokovic. Djoker ya yi godiya, musamman a fannin "karfin hali" Becker ya taimaka masa sosai saboda ya riga ya san irin wannan kalubale na rayuwa. Shi ma Becker ya amfana sosai saboda ya fita daga kanun labaran abin kunya.
Horaswa: A kai kasuwa
Djokovic da Becker sun yi murnar nasarori da suka samu. Karkashin jagorancin Becker, dan Sabiyan ya tattara jimillar kofin Grand Slam guda shida. Amma a cikin Disamba 2016, rabuwar abin mamaki ta biyo baya, inda Djokovic ya yi watsi da Becker. Dalili shi ne: Pepe Imaz na Spain, wanda ya cusa wa Djokovic wani sabon salon tunani da manufar "kauna da zaman lafiya".
Karayar arziki a 2017
Wata kotu a Landan ta ayyana Becker a matsayin wanda ya samu karayar arziki a watan Yunin 2017. Wani mai ba da bashi ya tabbatar da asarar miliyoyi. "Yana da wahalar yarda cewa na samu karayar arziki," in ji Becker. Wannan fatarar kudi ta dauki shekaru tana mummunan tasiri a kan kofuna da sauran abubuwa da ya mallaka. Cefanar da lambobinsa da aka yi ya samar da sama da Yuro 750,000.
Ya zama jami'in diflomasiyya
Domin kaucewa kulle-kulle, Becker ya yi ikirarin cewa shi ne wakili na musamman na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, don haka ya samu kariya. Shugaban kasar Faustin Archange Touadera (a hagu) bai amince da maganar nada mukamin jami'in diflomasiyya a hukumance ba. Gwamnati ta sanar da cewa fasfo din diflomasiyya da Becker ya gabatar na jabu ne.
Babban matsayi a tennis na Jamus
A tsakiyar 2017, an gabatar da Becker a matsayin mutum mai karfin fada a ji a tennis na Jamus: Ya rike sabon matsayi na "kocin mazaje" a hukumar tennis ta Jamus. "Ina son wannan wasa kuma ina kaunar wannan kasa. Ina farin cikin sake samun wani muhimmin aiki a wasan tennis a Jamus," in ji Becker. A cikin 2020 ya yi watsi da mukamin - saboda rashin lokaci, kamar yadda ya bayyana.