1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

AFCON: Boniface ba zai buga wa Najeria ba

January 9, 2024

Fitaccen dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayer Leverkusen ta Jamus Victor Boniface, ba zai samu damar buga wa kasarsa Najeriya wasa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ba a sakamakon raunin da ya ji.

https://p.dw.com/p/4b1ma
Hoto: INA FASSBENDER/AFP/Getty Images

Duk da cewa ba a yi cikakken bayani ba kan nau'in raunin da ya ke dauke da shi ba, amma dai tuni hukumar kwallon kafar Najeriya ta sanar da Terem Moffi da ke bugawa a Nice na faransa a matsayin wanda zai maye gurbin Boniface.

Tun da farko dai Najeriya da ta lashe kofin sau uku da za ta kara a rukuni daya da Côte d' Ivoire da Guinea-Bissau da Equatorial Guinea, ta raja'a kan Victor Boniface wajen taka rawar gani a gasar ta AFCON.

Idan za a iya tunawa dai, Boniface ya ci kwallaye akalla 10 da  hakan ya sa kungiyar ta Leverkusen, kasancewa gagara-gasa a saman teburin gasar Bundesliga a wannan kaka da ake ciki.

Sai dai a wasannin sada zumunci da ta yi, kasar Guinea ta lallasa Nigeria da ci 2-0, da wannan ke kasancewa kalulabe ga Najeriya na lashe kofin Nahiyar Afrika.