Boko Haram: Yara miliyan daya ba sa karatu
December 22, 2015
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rashin zuwa makaranta da yara ke yi a arewacin Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram ka iya taimakawa wajen haifar da karin masu tsaurin kishin addini.
Asusun dai ya bayyana hakan ne a wani sabon rahoto da ya fidda kuma hakan inji jami'in da ke kula da asusun a yammaci da tsakiyar Afirka Manuel Fontaine in yaran ba sa zuwa makarata, 'yan ta'adda ka iya sace su sannan su sanyasu a turbar da ba ta dace ba.
Kimanin makarantu 2000 ne wannan rikici ya sanya aka rufe su a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, yayin da dalibai sama da miliyan guda ba sa zuwa makaranta kana daruruwan malamai suka rasa ransu sakamakon rikicin.
Hukumomi a Najeriya dai sun lashi takobin kawo karshen tada kayar baya ta kungiyar ta Boko Haram a Najeriya. Rikicin dai ya yi sanadin rasuwar dubban mutane.