1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta yi wa garin Maiduguri da ke Najeriya kawanya

Yusuf BalaSeptember 11, 2014

Boko Haram na ci gaba da mamaya yankuna cikin daular da take ikirarin kafawa, abin da ya sanya manyan mutane daga yankin ke neman gwamnati ta kara dakarunta a arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1DAg9
Karte Nigeria

Mayakan Boko Haram sun yi kawanya ga garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma suna kokarin yin iko da garin a cewar wasu masu fada a ji daga yankin a ranar Alhamis dinnan. Dattawan sun bukaci a kara adadin yawan dakarun sojan Najeriya da ke a wannan yanki.

Wannan gargadi na manyan tsaffin jami'an gwamnati da tsaffin soji daga wannan yanki, na zuwa ne bayan da Amirka ta yi gargadin cewa ana iya kai hari a wannan birni, a yayin da masana a harkar tsaro ke cewa akwai fargabar gwamnati na iya rasa iko da yankin.

Birnin na Maiduguri na zama wani birni mai muhimmanci ga Kungiyar ta Boko Haram kasancewar wannan kungiya tushen ta ya tsiro ne daga wannan birni a shekarar 2002.

Har ila yau wannan kira na dattawan yankin na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar ta Boko Haram ta kwace wasu kauyuka da garuruwa a jihar ta Borno da Yobe da wasu sassa na jihar Adamawa, duka cikin yankunan da wannan kungiya ke ikirarin cewa nata ne cikin sabuwar daularta ta Islama.