Boko Haram Ta yi barazanar afkawa Jami'ar Maiduguri
July 11, 2011Hukumar kare hakkin bil adama ta tarayyar Najeriya ta bayyana cewar ta kaddamar da bincike kan zarge-zargen kisan ba gaira da aka yi wa shugabannin ƙungiyar Boko Haran shekaru biyun da suka gabata. Ita dai wannan hukumar ta ce ta yi wannan yunkuri ne dai domin a kauce wa fito na fito tsakanin gwamnati da 'yan boko haram da ya kai ga hallaka mutane da dama a garin maiduguri, tare da rufe jami'ar birnin daga wannan talatar.
A hannu guda kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu na tarayyar ta Najeriya sun fara bayar da shawarwari game da hanyoyin da ya kamata a bi domin warware taƙaddamar da ke tsakanin Boko Haram da kuma gwamantin tarayya. Wannan mataki na su ya biyo bayan ruɓanya hare-hare akan bayin Allah da ba su ji ba su gani ba da ƙungiyar ta Boko Haram ta yi a ƙarshen mako a wasu Garuruwa na arewacin Najeriya ciki kuwa har da Kaduna.Daga Najeriyar wakilammu na Abuja Ubale Musa da Kaduna Ibrahima Yakubusuka aiko mana da karin bayani.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu