Boko Haram ta kashe fararan hula 88 a Nijar
April 4, 2019MDD ta bayyana damuwarta dangane da halin da ake ciki a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar inda ta ce kungiyar Boko Haram ta halaka fararan hula 88 a watan Maris kadai a yankin Kudu maso Gabashin jamhuriyar Nijar a cikin jerin hare-haren da kungiyar ta zafafa wadanda kuma suka cilasta wa mutane sama da dubu 18 tserewa daga garuruwansu zuwa Diffa babban birnin yankin da wasu manyan kauyika na yankin.
A cewa Kungiyar kula da ayyukan jin kai ta MDD Ocha reshen birnin Yamai, kungiyar ta Boko Haram ta kai hare-hare 21 kan fararan hula da sojoji tare da kona gidaje kimanin 100 da yin awon gaba da mata masu yawa a yankin a cikin tsukin watan na Maris kadai.
Kungiyar ta kara da cewa yanzu haka mutanen da suka bar garuruwan nasu na ci gaba da kwararowa tara da tarewa a sansanoni dabam-dabam a yankin na Diffa. Lamarin da ta ce na kara haifar da barazanar tsaro a yankin na Diffa na yankin Tafkin Chadi