Kungiyar Boko Haram ta sake kai hari
May 15, 2015Talla
Rahotanni sun nunar da cewa maharan sun kai farmaki da misalin karfe uku na wannan Jumma'a a agogon Najeriya karfe biyu ke nan agogon GMT. Harin wanda aka kai a wajen birnin na Maiduguri a wani guri da aka sake tsugunar da mutanen da rikicin kungiyar ta Boko Haram ya tarwatsa da ke da nisan misalin kilomita 10 da garin na Maiduguri.
Kawo yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ko kuma suka jikata a wannan harin ba wanda ke zaman na biyu cikin wannan makon da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai a Maidugurin fadar gwamnatin jihar Borno.