Bobs 2016: Wasu 'yan Indiya sun yi nasara
May 2, 2016Yawan mutanen da aka kai wa hari da ruwan Acid a kasar Indiya ya karu da kashi 250 daga cikin dari daga shekara ta 2012 zuwa ta 2014. Akasarin wadanda lamarin ke shafa mata ne wadanda ruwan Acide din ke lalata masu fuska.
Wannan ce ta sanya hukumomin kasar ta Indiya suka kaddamar da wani kampe na neman kawar da wannan muguwar tabi'a ta kai hari da ruwan acide da aka yi wa lakabi "Stop Acid Attacks" ta hanyar faya-fayen bidiyo masu nuna fuskokin mutanen da aka kaiwa hari da ruwan na Acid.
Kampe din ya samu karbuwa kwarai a gurin al'umma tare da yin tasiri sosai wajen fadakar da su kan illar abin da muhimmancin yin watsi da tabi'ar harar mutanen da ruwan na Acid. Wannan kamfe na "Stop Acid Attacks" ya samu lambar yabo ta Bobs ta 2016 a fannin rawar da aikin jarida ke takawa wajen sauya tunanin al'umma.