Blinken ya kammala ziyarar kasashen Afirka
August 12, 2022Babban jami'in diflomasiyyar na Amirka ya isa birnin Kigali na Ruwanda a matsayin kasa ta uku a jerin kasashen da ya kai ziyara a Afrika. Blinken ya isa kasar Rwandan ne bayan tashe tashen hankula da aka fuskanta a gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango wanda ya jawo tabarbarewar dangantaka tsakaninta da makwabciyarta.
An zargin Rwanda da goyon bayan kungiyar yan tawayen Congo da ake kira M23 wanda ta dawo da fadan da suke yi shekarar bara bayan dakatar da shi na tsawon shekaru. Sai dai sakataren harkokin wajen na Amirka Anthony Blinken ya bukaci Ruwanda da kwango da su kai zuciya nesa
"Na tattauna kan batutuwan dake cewar Ruwanda na cigaba da mara wa kungiyar M23 baya kuma tana da nata Jami'an a jamhuriyar dimokradiyar kongo. Mun san cewa Rwanda na da tata matsalolin tsaron, Sako na zuwa ga shugaban kasa Tshisekedi da shugaban kasa Kagame, duk wani goyon baya ko hadin gwiwa da yan ta'adda a kongo zai jefa yankuna da dama cikin hadari da rashin zaman lafiya.
Kungiyar kare hakkin bil Adam ta Human Rights Watch ta nemi Blinken ya jan hankali akan tauye hakkokin yan Adam da ake yi a Ruwanda wanda ya hada da daukar mataki kan wadanda suka saba doka. Saboda haka Mista Blinken bai yi kasa a gwiwa ba wajen kira ga gwamnatin Rwanda da ta mutunta hakkin 'yan adawa
Daya daga cikin burin Blinken a Rwanda shine sanya jami'an gwamnati a batun Paul Rusesabagina wani dan kasar Amurka wanda ake tsare da shi a gidan yari bayan yanke masa hukunci kan zargin ta'addanci batun da ya jawo cece kuce.