Karin rigakafin corona na uku
November 30, 2021Firaminista Boris Johnson ya ce za a bude runfunan yin karin rigakafin a lungu da sako na kasar a wannan satin. Jonson ya ce nan da karshen watan Janairu suna fatan yi wa duk wanda ya yi rigakafin karin na 3.
Birtaniya na zama daya daga cikin kasashen duniya da cutar corona ta fi yi wa barna, A shekarar da ta gabata sama da mutum dubu dari da arba'ain ne corona ta yi sanadiyar rayukansu a kasar. Yanzu haka an sami mutane 13 dauke da wannan sabon nau'i na Omicron da wasu mutum 9 daga yankin Scotland. Ministan lafiyar kasar ya ce duk alamomi na munamusu za a sami karuwar mutane dauke da sabon nau'in a ranakun da ke tafe.
Kasar na samun karuwar masu kamuwa da cutar da sama da kaso 80 cikin dari, daga cikinsu yara ne masu shekaru 12 da kuma wadanda tuni suka riga suzka yi rigakafin.