Iyakar Jamus da Birtaniya za ta kasance a rufe
December 20, 2020Majiya daga ma'aikatar lafiyar Jamus na cewa, yanzu haka hukumomin kasar na ci gaba da tattauna batun rufe iyakar da Birtaniya ta sama da ta jiragen kasa, duba da fargabar da ake fuskanta na yaduwar sabuwar cutar ga jama'a.
Idan har Jamus din ta kai ga daukar wannan mataki, hakan na nufin ta bi sahun kasar Holland wacce ita ma a yau Lahadi ta bayyana rufe kofofinta na sama ga kasar ta Biraniya wacce ke fuskantar bullar sabuwar kwayar cutar ta COVID-19 sabon samfuri, wanda kawo yanzu likitoci suka kasa kai ga ganowa.
Tuni ita ma kasar Beljiyam ta bayar da sanarwar rufe iyakokinta da Birtaniya ta sama da ta jiragen kasa tun daga yau Lahadi har tsawon kwanaki biyu kamar yadda wani kusa a gwamnatin ya sanar.
Ko a ranar Asabar din da tagabata dai, firministan Birtaniyan Boris Jonhson ya ce sabon nau'in kwayar cutar da ya mamayi Landan, na da saurin yaduwa fiye da wanda aka sani a baya da kaso kimanin 70 cikin dari