Bukatar rufe majalisar dokokin Birtaniya na wucin gadi
August 28, 2019Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya mika wa Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu bukatar a dakatar da aikin majalisar dokokin kasar daga tsakiyar watan Satumba zuwa tsakiyar watan Oktoba. A tsukin wannan lokaci ba za a shirya wani zama a majalisar ba.
Masu adawa da ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai EU ba tare da yarjejeniya ba, sun takaita lokacin, a wani mataki na amfani da doka don hana Birtaniyar ficewa daga EU a ranar 31 ga watan Oktoba ba da yarjejeniya ba. Sai dai Firaminista Johnson ya yi watsi da zargin da aka yi cewa yana son yi wa majalisar dan-waken zagaye ne a takaddamar da ake yi game da shirin ficewar.
Kakakin majalisar dokokin Birtaniya, John Bercow ya bayyana matakin na Firaminista Johnson da cewa ya karya dokar tsarin mulkin kasar.
A nata bangaren Hukumar Tarayyar Turai a ta bakin mai magana da yawunta, Mina Andreeva ta ce ba za ta tsoma baki a cikin batun ba. Ta ce EU ba ta tsokaci kan batutuwan siyasa na cikin gida na kasashe membobinta.