Binciken ICC kan rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
February 7, 2014Talla
Bensouda ta ambata hakan ne a wannan Juma'ar inda ta ce sun yanke shawarar fara binciken ne saboda halin da ake ciki musamman ma dai kashe-kashe da kuma wasu batutuwa na tauye hakkin bani adama a kasar sun wuce gona da iri.
Babbar mai gabatar da karar ta ce wani abu da ya zaburar da su wajen yin bincike shi ne irin rahotannin da suka samu dangane da irin cin zarafin jama'a da kungiyoyi daban-daban ke yi a kasar tun da aka fara rikici mai nasaba da kabilanci da addini a kasar a watannin da suka gabata.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu Waba