Bikin ranar Mandela a duniya
July 18, 2010A yau ne shugaban 'yan gwagwarmayar ƙwatan 'yancin baƙaƙen fatan Afirka Ta Kudu kuma baƙar fata na farko da ya shugabanci ƙasar Nelson Mandela yake cika shekaru 92 a duniya. Domin gudanar da wannan biki dai yanzu haka an umarci al'umar ƙasar Afirka Ta Kudun da ma sauran ƙasashen duniya su gudanar da aiyukan taimakon kai da kai na mintuna 67, kwatankwacin shekarun da ɗan kishin ƙasar ya shafe yana gwagwarmayar siyasa a rayuwarsa, domin girmama shi.
A yayin da shi kuma Mandela, wanda yanzu haka ya tsufa tukuf zai gudanar da bikin ne a gidansa tare da iyalai da wasu yara 100 da za'a kwaso daga mahaifarsa ta Mvezo dake gabashin lardin Cape zuwa birnin Johannesburg.
Kamfanin dillancin labaran Jamus ya ruwaito shima shugaba Jacob Zuma tare da sauran 'yan siyasar ƙasar za su garzaya zuwa mahaifar Mandelan domin gudanar da nasu aiyukan gaiya na gina wani ɗakin shan magani.
Majalisar Ɗinkin Duniya ne dai ta ware ranar 18 ga Yulin kowace shekara domin fara gudanar da bikin ranar tunawa da Nelson Mandela da nufin girmama wannan dattijo da ya sadaukar da rayuwarsa domin samun 'yancin baƙaƙen fata a ƙasarsa da ma duniya baki ɗaya, gwagwarmayar da kuma ya kawo ƙarshen salon mulkin wariyar launin fata a Afirka Ta Kudu.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Mohammad Nasiru Awal