Bikin cikar Mandela shekaru 95
July 18, 2013Talla
A shekaru 2010 MDD ta ayyana rana a matsayin ta Mandela domin tunawa da irin ayyukan da ya yi. An shirya za a ware mintoci 67 don ayyukan gayya a Afirka ta Kudun domin girmama shekaru 67 da Mandela ya yi na sadaukar da rayuwarsa.
Kawo yanzu jama'a a ƙasar yara da manya kowane na yi wa Madiban fatan samu ƙarin lafiya a wannan rana. Wanda a yau ya shafe kusan makonni shida a asibiti ana yi masa magani saboda rashin lafiyar da ya ke fama da ita. Duniya na ci gaba da yi masa fatan alheri tare da gudanar da ayyuka na gari.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu