Biden da Trump sun yi fintinkau a "Super Tuesday"
March 6, 2024Wannan zabe na 'Super Tuesday' zai ba da damar yakin karshe tsakanin tsohon shugaba Trump da shugaba Mai ci Biden a zaben shugaban kasa na 7 watan Nuwamban 2024.
Karin bayani:Kotun Illinois ta cire sunan Donald Trump daga cikin zaben fitar da gwani takarar shugaban kasa
A jawabin da ya gabatar gaban dandazon magoya bayansa a harabar gidansa da ke Florida, Mr. Trump na jam'iyyar Republican ya bayyana ranar a matsayin daren alkhairi mai cike da ban al'ajabi. Trump ya kuma soki Biden kan manufofinsa da suka shafi shige da fice a iyakar Mexico, inda ya bayyana su a matsayin aikin 'Baban giwa".
Karin bayani:Donald Trump da Hillary Clinton sun yi nasara
Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito cewa Nikki Haley da ke kasancewa 'yar takara daya tilo da ke hamayya da Trump a zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican ta yi nasara a jihar Vermont.