Batun ceto Euro ya samu targaɗe
October 12, 2011Majalisar dokokin ƙasar Silovakiya ta kasa amincewa da kuri'ar da za ta samar da wani asusun ceto kuɗin Euro. Hakan yana nufin tsarin da ƙasashen Turai suka yi na samar da asusun da zai agazawa ƙasashen da suka kasa ba zai fara aiki ba. Domin kuwa kafin kudurin ya fara aiki dole sai dukkan ƙasashe 17 dake amfani da kudin Euro sun kaɗa kuri'ar amincewa da shi. 'Yan majalisa 55 biyar ne kacal daga cikin 124 hudu dake zauren majalisar lokacin kada kuri'ar suka yi na'am da shirin. Firai ministar ƙasar Bratislava Iveta Radicova ta ce rashin kaɗa ƙuri'ar tamkar faɗuwar gwamnatinta ne. Za dai a kada ƙuri'ar zagaye na biyu inda gwamnati za ta nemi goyon bayan 'yan adawa. Manufar kuɗurin dai shine a samar da wani asusun ko ta kwana wanda zai riga tallafawa duk wata ƙasar da a ka ga ta kasa a fannin tattalin arziki
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu