1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun aikewa da dakaru zuwa iraq ya fara fuskantar matsala

Mansour Bala BelloAugust 5, 2004

Bukatar da kasar saudiya tayi na kasashen musulmi su fara aikewa da dakarun tsaro a can Kasar Iraq ya fada wani irin wadi na tsaka mai wuya .Pm iyad Allawi na kasar dake kada kugen cimma wannan mataki ya fuskanci koma baya a inda kasashen ke dar dar da batun .

https://p.dw.com/p/BvhX
Hoto: dpa

iyad Allawi dai ya bukaci hakan ne a makon daya gabata a yayin daya gana da sakataren harkokin kasashen ketare na Amurka kolin Powella kasar saudiyya .Yace a bisa halin rayuwa da ake fuskanta a yanzu haka a kasar ta iraq akwai bukatar samun dakaru daga kasashen musulmi domin cimma wannan manufar da aka sanya a gaba .Yace da fatan dai kasashen musulmi ba zasu razana ba bisa yawan rahotanni na yin garkuwa da yan kasashen ketare a kasar ba .To sai dai nan take kasar masar tayi adawa da batun .Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Ahmed Abdulgheit yace ko kadan kasar ba zata tura dakaru ba a iraq kuma kota halin kaka .Ya dai tabbatar da hakan ne a yayin da ministan ya gana da shugaban Kasar Hosni mubarak jim kadan bayan sanarwar wannan batu a kafafan yada labaru .To sai dai yawancin kasashen larabawa sun soki wannan lamirin da cewa ba abu ne da zai sabu ba .Bugu da kari kasashen dai na cikin dar dar bisa tsoron fantsamar rikicin zuwa sauran kasashen musulmi musamman mAkwabta da iraq ..Idan dai baa antaba a makon daya gabata shugaba Muammar gadaddafi ya bukaci sauran kasashen musulmi da kada su fara tura dakaru cikin kasar ta iraq kamar yarda Pm Iyad Allawi ya bukata ..Tun ba yanzu ba dai Kasashen musulmi suka bayyana raayin su cewa zasu shiga Iraq bisa laimar mdd .Yawancin gwamnatin kasashen musulmi dai na kallon lamarin tamkar bata sake zane ba a dangane da kutsen da Amurka tayi a kasar ta iraq .A yanzu dai kamar yarda kakakin kungiyar kasashen larabawa Hasan Zaki yace bisa bukatar da Saudiyya ta gabatar na aikewa da dakaru daga kasashen musulmi har kawo yanzu babu wata kasa da aka tuntuba kann wannan batun ..To sai dai duk da wannan bukartar da saudiya ta gabatar har yanzu bata tura koda Soji daya ba a kasar ta iraq ..Wata majiya dai na cewa inda gizo ke sakar itace koda kuwa an aike da wadannan dakaru wace kasa ce zata ja ragamar dakarun .? wannan itace tambayar da Amurka ta gabatar a dangane da wannan aniya ..Cikin kasashen dai da suka nuna aniyarsu ta wannan fuska sun hadar da Pakistan Yemen Algeria da Tunisia domin tattabbatar da tsaro a kasar ta iraq .To sai dai idan baa mantaba a makon daya gabata wasu yan tsageru a kasar ta iraq suka kashe yan kasar Pakistan su biyu wadanda ke aiki a wani kanfani mallakar kasar Kuwait a iraq wanda ya dada dagula alamurra a tsakanin bangarorin biyu .Wata majiya dai na cewa yawancin yan kasar ta iraq na nuna adawa da wannan batu na aikewa da dakaru daga kasashen musulmi da abun da suka kira da cewa zasu kasance yan amshin shatan Amurka A cewar daya daga cikin manyan Sojin kasar ta iraq dayayi ritaya Abu talat yace wanan batu dai wata makrkashiya da Kasar Isreala ta shimfidawa kasar ta Amurka domin a sami wata kafa na rarraba kawunan musulmin duniya ..Binciken dai ya nunar da cewa daga kann shiawa da Kurdawa da yan darikar sunni na adawa da wannan shirin na Iyad Allawi Pm kasar da kuma iyayen gidansa wato Amurka da Britaniya .