Basco Ntaganda da lauyoyinsa sun bada ba`asi
September 3, 2015
A rana ta biyu ta sauraren karar tsohon madugun Yan tawayen dai Basco Ntaganda da ake yiwa lakabi da "Terminator" ya musanta irin zarge-zargen 18 da ake yi masa, yayin jawabinsa na mintuna tara, wadanda suka hada da cin zarafin jama'a da fyade da gallazawa, tare da tilastawa yara kanana shiga ayyukan soji. Inda maimakon hakan ya bayyana cewar ya yi iya bakin kokarinsa wajan bayar da kariya ga jama`ar da ake zargin wai yaci zarafinsu.
Har ila yau tsohon madugun yan tawayen, ya musanta zargin da ake masa na cewar zai gabatar da wasu shaidun bogi wadanda za su kare shi. Al´amarin da lauyoyinsa suka ce masu shigar da kara kan tuhumar da ake yi masa basu da wata kwakkwaran hujjar da za su kama shi da laifi.
Ko da a ranar Larabar 02.09.2015 da aka fara shari`ar ma, sai da mai shigar da kara ta kotun ICC Fatou Bensouda, ta kira shi a matsayin sojan da ya zura ido sojoji suka yayyanka mutane, ba tare da ya tsawatar musu ba.