1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barnar ambaliyar ruwa a Indiya

Yusuf BalaAugust 22, 2016

A jihar Bihar da ke a Gabashin Indiya an kwashe mutane 60,000. Yayin da ake fargaban karuwar ambaliyar cikin kwanaki da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1Jn6h
Überflutung Flut in Indien
Hoto: Getty Images/S.Kanojia

Akalla mutane 40 ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa a wasu yankuna na tsakiya da gabashin Indiya, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Litinin din nan.

Kwanaki da aka dauka ana maka ruwan sama mai karfin gaske, ya sanya kogin Ganges ya tumbatsa da ma yin ambaliya, abin da ya shafi larduna kimanin 20 na jihohin Madhya Pradesh da Bihar da Uttar Pradesh. A garin Allahabad da kogin na Ganges ya ratsa kimanin mutane 12,000 ne aka nemi su kauce daga inda suke zaune. A jihar Bihar kuwa an kwashe mutane 60,000. Yayin da ake fargaba ta karuwar ambaliyar cikin kwanaki da ke tafe.