Yiwuwar rikicin kasuwanci da Amirka
June 1, 2018Kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki na dab da fadawa wani yakin kasuwanci gadan-gadan a daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Kanada da Mexiko suka yi barazanar daukar matakan fansa kan gwamnatin Amirka wadda a wannan Jumma'a ta fara aiwatar da sabon kari na haraji da ya kai kashi 25 cikin 100 da kuma na kashi 10 cikin 100 kan karafa da goran ruwa da wadannan kasashen ke shiga da su Amirka.
Dukkan kasashen da abin ya shafa da suka hada da na kungiyar tarayyar Turai EU da Kanada da kuma Mexiko sun fusata dangane da wannan mataki na karin harajin kayan da ake shiga da su Amirka musamman na fannin karfe da goran ruwa da gwamnatin Amirka karkashin Shugaba Donald Trump ta fara aiki da shi a wannan Jumma'a.
Tuni dai kungiyar EU ta ce za ta kalubalanci wannan mataki a gaban kungiyar ciniki ta duniya wato WTO. Jami'ar kula da harkokin ketare ta EU Federica Mogherini ta fada a birnin Brussels cewa dole ne kungiyar ta kare muradunta, inda ta kara da cewa za a kara kudin kwasta na wasu jerin kayayyaki da Amirka ke shigowa da su kasashen EU amma ta kara da cewa hakan ba ya nufin cewa Amirka ba za ta ci gaba da zama babbar kawa ta Tarayyar Turai ba.
Har zuwa wannan lokaci dai kasashen na Turai dai sun yi fatan Amirka za ta janye su daga sabbin kudaden na kwasta, domin a duk shekara suna sayar wa Amirka karafa da nauyinsu ya kai tan miliyan 3.5. Amma duk tattaunawar da aka yi tsakanin EU da Amirka sannan daga baya a kungiyar hadin tattalin arziki da ci-gaba a birnin Paris bisa wannan manufa sun ci-tura.