Barazanar annobar kwalara a Nijar da Najeriya
December 3, 2015Hukumar lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta yi gargadin yiwuwar fuskantar annobar kwalara a kasashen Afirka da dama a shekara ta 2016. Wakilin Hukumar ta WHO a Nijar Assimawe Pana ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban taron kwararrun likitoci na kasashe Afirka 17 da ke gudanar a yanzu haka a birnin Yamai na jamhuriyar ta Nijar.
Wakilin Hukumar ta WHO ya ce binciken da hukumar tasu ta yi ya nunar da cewa mutane kimanin miliyan 500 na tun daga yankin kasar Senegal a Afirka ta Yamma har zuwa kasar Ethiopia a yankin Gabashin Afirka na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalarar a shekarar mai kamawa ta 2016.
Sai dai ta ce hadarin ya fi kamari a kasashen Nijar da Najeriya wadanda dama suka yi fama da ita a wannan shekara ta 2015 inda ta halaka mutane 573 a Nijar din da wasu 557 a makobciyarta ta Najeriya