1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankwana ga gawar Nelson Mandela

December 11, 2013

An ajiye gawar Mandela a birnin Pretoria inda mutane suka fara bankwana na ƙarshe a tsawon kwanaki uku.

https://p.dw.com/p/1AXKt
Nelson Mandela Abschied 11.12.2013
Hoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Hukumomin Afirka ta Kudu sun ajiye gawar ɗan gwaggwarmayar yaƙi da wariyar launin fata Nelson Mandela a ginin Union Building da ke birnin Pretoria domin bai wa al'umma damar yin bankwana da marigayin. Za a bar gawar ta Mandela har tsawon kwanaki uku a cikin ginin da ya yi rantsuwar kama aiki lokacin da aka zaɓeshi a matsayin shugaban Afirka ta Kudu.Dangin marigayin da kuma manyan baƙi daga ƙasashen ƙetare za su fara tururruwa kan gawar ta Mandela kafin daga bisani a bai wa 'yan ƙasar damar bankwana da shi. A ranar lahadi ne dai za a binne Mandela a ƙauyensu na Qunu a lardin Cap ta Gabas.

Dakarun Afirka ta Kudu ne suka ɗauko gawar Mandela da aka naɗe da tutar ƙasa a kan keken doki har i zuwa farfajiyar ginin haɗin kai na Pretoria. Da ma dai tun a ranar Talata darurruwan mutane da kuma shugabannin ƙasashen duniya sun halarci bukin karrama Mandela da ya taɓa lashe lambar yabo ta zaman lafiya. Shi dai baƙar fatan na farko da ya shugabanci Afirka ta Kudu ya mutu ne a ranar Alhamis da ta gabata bayan da ya shafe shekaru 95 a duniya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu