1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bankuna sun samu riba mai yawa

October 7, 2024

A yayin da tattalin arzikin Tarayyar Najeriya ke cikin wani hali, bankunan kasar a halin yanzu na kirgar riba mara adadi. Can a zahirin rayuwar yau da gobe dai, tattalin arzikin kasar yana ji a jikinsa.

https://p.dw.com/p/4lVr6
Najeriya | Banki | CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Sakamakon manufofin jari hujjar da ke tasiri a tsakanin miliyoyin 'yan kasar ne dai, al'umma ke ta kukan babu. Wani rahoto dai ya ce manyan bankunan kasar 11 sun samu ribar da ke da girman gaske, a cikin watanni shidan farkon shekarar bana. Naira triliyan uku da biliyan 7000 ne dai, bankunan suka samu a cikin sunan riba daga watan Janairu zuwa na Yunin bana. Adadin kuma da ya haura sama da kaso 100, na yawan ribarsu a farkon watanni shidan shekarar da ta shude. Tuni dai samun ribar bankunan ke daukar hankali a Najeriyar, inda bankunan suka yi kaurin sunan hada baki wajen zagon kasa ga tattalin arzikin kasar. Dakta Surajo Yakubu dai kwarrare ne a binciken laifukan kudi, kuma ya ce bankunan suna da jerin tambayoyin amsa wa kan hanyar samun kudin a dare daya.

Nijar: Kwarara 'yan Najeriya a Maradi

Karuwar arzikin bankunan Najeriyar dai, na zuwa a lokacin da babban bankin kasar ya nemi kara yawan hannun jarin bankunan da nufin kauce wa tangal-tangal da kila ma rushewar da kudin al'umma. Bankuna kusan uku ne dai, a kasa da watanni uku bankin na CBN kai ga korar jami'an tafi da su da nufin ceton dukiyar da ke a cikinsu. To sai dai kuma arzikin dare dayan a tunanin Ibrahim Shehu da ke zaman sakataren kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Arewacin kasar, na da ruwa da tsaki da sabon yanayin kudin da Najeriya ke fuskanta yanzu. Tarayyar Najeriyar dai na zaman ta kan gaba cikin batun kudin ruwa, inda bankunan ke karbar kaso 35 cikin 100 da sunan kudin ruwa a basussukan da suke bai wa masu bukata amma kuma ke biyan ruwan kaso biyar cikin 100 cikin kudin ajiya na mutane. Wannan bambancin dai, na da girman gaske da kuma tarnaki ga kokarin samun bashi a bankunan kasar.