Hasashen raguwar matsanancin talauci a duniya
October 7, 2015Hasashen na Bankin Duniyar ya kuma yi nuni da cewar samun raguwar talaucin da kashi 28 cikin 100 nan da karshen shekara ta 2015 wata babbar alamar nasara ce wajen kawar da talauci nan da shekara ta 2030 a duniya.
A yayin da yake maida martani a kan hasashen rahoton Bankin Duniyar, Jim Yong Kim da ke zama Shugaban Bankin nuni yayi da cewar hasashen abin karfafa gwiwa ne kuma suna cikin sahun farko na tarihin wannan karnin da zai kai ga kawo karshen matsalar fatara da taluci a duniya baki daya.
To sai dai Bankin Duniyar ya yi farat ya yi gargadin cewar lallai ne akwai gagarumin aiki a nan gaba. Philip Schellekens da ke zama babban jami'i a bangaren tattalin arziki kana kuma babban marubucin alkalumman tattalin arzkin duniya da ke a Bankin ya ce.
"Har yanzu kalubalan na karuwa duk kuwa da irin gagarumin cigaban da ake samu ta irin yadda muka yi hasashen a tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2015, koda yake muna ganin akwai yiwuwar matsalar ta kara yin kasa."
Dalili daya dai shi ne ragowar wadanda ke fuskantar matsalar talaucin na da wuya a kai gare su.
Shin wane ne ya fi fama da matsanancin talauci?
Bisa kididigar auna mizanin wadanda ake wa kallon suna tattare da matsanancin talauci na Bankin Duniyar su ne wadanda ke rayuwa da kasa da Euro 1.70 a kowace rana ta Allah.
Bankin dai na yin aiki ne da kididdigar da ya yi ta baya kan dalar Amirka 1.25 a shekara ta 2005.
Bugu da kari wannan dai ba yana nuni da cewar mizanin talaucin da aka auna ya yi sama ba ne. A'a sai dai alkalumman ne kawai aka dai-daita ta yin la'akari da sauye-sauyen tsadar rayuwa a tsakanin kasashe 15 masu tasowa a duniya. Kazalika Schellekens ya kara da cewar:
"Sabon mizanin auna tsananin talauci a bayyana yake, ta yin duba da tsohon mizanin. A duk bayan shekaru biyar a kan sabunta canjin da ake amfani da shi. Don haka muna bukatar wannan canjin ta yadda za mu auna yadda zai kai wajen sayan muhimman bukatun jama'a wanda zai nuna a fili yadda talaucin yake."
Daidaituwar manufofin ita ce mafita
To amma Deborah Hardoon mataimakiyar shugaban sashen bincike a kungiyar agaji ta Oxfam da ke birnin London ta ce sam-sam wannan ma'anar ba ta yi dai-dai da kowa ba ta kuma ci gaba da cewar.
"Talauci ya fi gaban nan, kana kuma matsala ce mai girman gaske. Don kana da dala 1.90 ba ya nufin kai ba mataluci ba ne. Wannan shi ne mafi kankanta kuma shi ne yake a tsakanin kasashe 15 masu tasowa a duniya, a inda aka yi itifaki cewar mutum zai rayu, zai ci abinci kana ya yi wasu abubuwa da zai tafiyar da rayuwarsa cikin sauki."
Koma dai mene ne hasashen da Bankin Duniya ya yi na cewar yawan adadin mutanen da ke fama da talauci ana sa ran zai ja baya daga adadin mutane miliyan 902 a shekara ta 2012 zuwa miliyan 702 nan da karshen shekara ta 2015, wanda hakan ke zama babbar nasara, za ta kai ga kawar da talauci kwatakwata nan da shekara ta 2030. A yayin da Bankin Duniyar ya yi nuni da cewar dole ne a samu daidaituwar manufofi a tsakanin kasashen duniya musamman kasashen Afrika Kudu da Sahara, da a nan ne matsalar ta fi kamari da kashi 50 cikin 100.