1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban ya ja hankalin yan takara a Gabon

Abdullahi Tanko BalaAugust 30, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kwantar da hankula a Gabon yayinda ake jiran sakamakon zabe.

https://p.dw.com/p/1Jsj3
Griechenland Besuch UN Generalsekretär Ban Ki-moon
Ban Ki Moon: Sakataren Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Getty Images/AFP/Y. Kontarinis

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya tattauna ta wayar tarho da yan takarar shugabancin kasar Gabon inda ya bukacesu da su umarci magoya bayansu su nuna halin dattako da sanin ya kamata yayin da ake jiran fadin sakamakon zaben da aka gudanar.

Ban ya yi magana da shugaba mai ci Ali Bongo da babban mai kalubalantarsa Jean Ping, wadanda dukkanin su suka yi ikrarin lashe zaben tare da zargin juna da yin magudi bayan zaben na ranar Asabar.

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya baiyana damuwa kan yadda yan takarar kowanne ya ayyana samun nasara tun gabanin an baiyana sakamakon a hukumance.

Akwai dai fargabar cewa mai yiwuwa a sami barkewar tashin hankali makamancin abin da ya faru a lokacin zaben 2009.

Ban Ki Moon ya bukaci yan takarar biyu su sulhunta duk wata takaddama a kan zaben a gaban kotu maimakon tada hankali.