Ban Ki-Moon ya isa birnin Juba a Sudan ta Kudu
February 25, 2016Talla
Yayin isowar sa a kasar ta Sudan ta Kudu sakataran na Majalisar Dinkin Duniya ya samu tarbo a filin jirgin sama na Juba babban birnin kasar daga Ministan harkokin wajan kasar Barnaba Marial Benjamin kafin daga bisani ya gana da shugaban kasar Salva Kiir inda za su tattauna batun yakin basasan da ya daidaita kasar tun daga watan Disamba na 2013, da kuma batun aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Augusta na 2015 tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a kasar.
Ana sa ran batun harin da aka kai na ranekun 17 da 18 ga wannan wata na Febrairu a sansanin 'yan gudun hijira na Malakal da ke karkashinMajalisar Dinkin Duniya zai shigo cikin tattaunawar.