Ban Ki Moon ya fara ziyarar aiki ta farko a Kongo
January 27, 2007Talla
Babban sakataren MDD Ban Ki Moon yayi kira ga gwamnatin JDK da ta kulla wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin al´umar kasar da kuma gamaiyar kasa da kasa. Ban wanda ya isa Kongo a wata ziyarar aiki ta farko a wajen tun bayan hawarsa kan kujerar sakatare janar na MDD, ya yiwa majalisar dokokin Kongo jawabi bayan ya gana da FM. Ban ya ce ba za´a iya yin watsi da batutuwan kare hakin bil Adama da aikin sake gina kasar ba, muddin ana son zaman lafiya da demukiradiyya sun wanzu a Kogon. A wani lokaci yau Ban zai gana da shugaba Josef Kabila kana daga bisani ya kaiwa dakarun MDD ziyara. MDD ta girke dakarun kiyaye zaman su dubu 18 a kasar ta Kongo.