Bama-bamai sun kashe mutane 58 a Maiduguri
March 7, 2015Hukumomin Kiwon lafiya na jihar Borno ta tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 58 yayin da dama suka jikata, bayan tashin wasu tagwayen bama-bamai a birnin Maiduguri fadar gwamnatin wannan jiha. Cikin mintuna arba'in ne dai bama-bamai uku suka tashi a ranar Asabar a babbar mashigar kasuwar kifi da ke tashar Baga da kuma kusa da Post Ofis na babbar kasuwar Maidugiri da ake kira Monday market.
Wadanda suka shaidar da lamarin suka ce maharan sun aiwatar da danyen aikin ne da wasu motoci da ke dauke da bama-bamai, wadanda tun da farko aka nuna shakku a kansu. Babu dai kungiya da ta yi ikirarin kai wadanda tagwayen hare-haren. Amma kuma sun yi kama da wadanda Kungiyar Boko haram da ke neman kafa daular musulunci ke kaiwa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Masu aikin ceto na ci gaba da kulawa da wadanda bama-baman suka ritsa da su a hare-haren na Maiduguri.