Bala'in ambaliyar ruwa a Spain: Shara bayan hukuba
Mako guda bayan ta'adin ambaliyar ruwa a gabashin Spain, ana ci gaba da neman masu sauran nunfashi. An samu nasara amma ana ci gaba da neman mutanen da bala'in ya ritsa da su. Babu tabbacin yawan mutanen da suka bata.
Amfani da amlanke wajen kwashe tabo
Bala'i iya ganin ido. Mako guda bayan ambaliyar ruwa a gabashin Spain, mazauna yankin da masu aikin ceto suna kokarin sake samar da hanyoyi a yankin Valencia. Kimanin 'yan sanda dubu-17 da masu kashe gora da sojoji suke ci gaba da neman masu rai da suka bace. Kimanin mutane 218 suka mutu sakamakon bala'in kuma ana kara samun wadanda mutu.
Mutuwa a wajen ajiye motoci a karkashin kasa
Kamar wani fim na nuna abin tsoro: Ranar Litinin jami'an kasar Spain sun binciki wajen ajiye motoci karkashin kasa da reuwa ya mamaye sakamakon ambaliya. Yanzu haka an karfafa neman mutanen da suka bace a karkashin kasa wajen ajiye motoci, inda ya zama tamkar tarkon mutuwa. Masu nunkaya suna cikin masu aikin taimakon.
Nema cikin firgici
Ana ci gaba da neman mutanen bayan gini ya rushe kansu. Babu alkaluma a hukumance na mutanen da suka bace. A cewar ministan sufuri na kasar Oscar Puente, wanda ya ce akwai wuraren da ruwan ruwa ya mamaye cikin gine-gine gami da karkashin kasa wuraren ajiye motoci inda ake ci gaba da aikin ceto. Sannan ya kara da cewa akwai kuma wadanda suka mutu a wuraren.
Aiki tare
A garin Paiporta, wanda ambaliyar ruwa ta fi tagaiyarawa, masu aikin taimako na sa-kai suna hada hannu wajen daukan bukitoci suna yashe tabo. Akwai kuma kasadar kara samun weuraren da za su rushe. Galibi masu aikin taimakon sun sanya kyallen kariya na hanci.
Tabo a jikin Sarki
Mazauna yankin da aka samu ambaliyar ruwan sun fusata lokacin da Sarki Felipe yake ziyara kan bala'in da aka fuskanta inda suke cewa ya "fice" tare da Firaminista Pedro Sánchez da kuma jagoran yankin Carlos Mazón, inda aka watsa musu tabo. Galibin mutanen sun yi zargin gwamnati ta yi watsi da su.
Taimako a karshe!
Wata mazauniyar yankin ta rungumi soja domin nuna jin dadin taimako ya iso. Mutane da dama a kasar Spain sun mamakin jinkirin da aka samu kafin tura sojoji taimakon mutanen yankin da aka samu bala'in. Akwia kuma sukar gwamnatin ynakin Valencia da ake yi na rashin tura sakonnin gaggawa ta wayoyin tarho har sai bayan sa'o'i 12 da samun ambaliyar ruwan.
Kokari cikin tabo
'Yan sanda suna aikin kawar da tabo a titin Alfafar, kusa da garin Valencia. Wasu garuruwa da suka yi fice a wajen yawon shakatawa sun kara sake samun ruwan sama cikin sa'o'i kalilan kamar yadda suke samu a shekara. Ana sa ran hsare wuraren zai dauki makonni. Sannan sake gina wuraren mai yuwuwa zai dauki shekaru.
Nasarar farko
Tsaunuka da shara gami da tabo: Bugu da kari masu aikin ceto da dubban ma'aikatan sa-kai suna taimakawa wajen tsabtace yankin. Nasarar farko ita ce an dawo da kusan daukacin hasken wutar lantarki. Hanyoyin mota da na jirgin kasa ana kyarawa sannu a hankali, sannan an dawo da kaso 60 cikin 100 na layukan tarho.
"Zahirin sauyin yanayi"
Motocin da suka lalace a Valencia. Guguwa mai karfi ta saba ratsa yankunan Spain, amma masu bincike sun amince cewa sauyin yanayi na kara tabarbara halin da ake ciki. Ursula von der Leyen shugabar hukumar gudanar Tarayyar Turai ta yi gargadin cewa zahirin sauyin yanayi abu ne da tilas a shirya masa.